A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, Ayatullah A'arafi ya yi nuni da halin da ake ciki a yanzu, inda ya bayyana shi a matsayin "marar misaltuwa," kuma ya ce bayan "Dufanul Aqsa" da kuma abubuwan da suka faru kwanan nan, an rubuta wani sabon babi a tarihi. Ya kara da cewa a matakin kasa da kasa, muna shaida hadin gwiwar dakaru daban-daban kamar gwamnatin Sahyoniya, Amurka, Turai, da wasu kasashen Larabawa wadanda ke tafiya don cimma manufofi guda, wanda hakan ke nuna manyan kalubale ga Juyin juya halin Musulunci.
Shugaban Makarantun Hauzar ya bayyana cewa abin da ya banbanta wannan zamani shi ne goyon baya da hadin gwiwar al'ummar duniya marar misaltuwa ga nazariyyar Juyin juya halin Musulunci, kuma ya jaddada cewa wannan yanayi, a lokaci guda yana kawo manyan damammaki da barazana ga cibiyoyin addini da na juyin juya hali, musamman ma makarantun addinin.
Ya bayyana mamayar al'adun Yamma a matsayin daya daga cikin manyan barazana, yana mai cewa Juyin juya halin Musulunci ne kawai juyin juya halin da ke tsaye sosai a gaban fadada wayewar Yamma tsawon karni hudu zuwa biyar. Bugu da kari, ci gaban fasaha cikin sauri, musamman a fannin ilimin wucin gadi (AI) da ilimin fahimta, sun samar da wasu kalubale biyu da ke bukatar sabon tsari mai kuzari daga cibiyoyin addini da makarantun Hauza.
Ayatullah A'arafi ya jaddada bukatar shiri, hangen nesa, da kuma samun dabarun hadin kai kuma ingantattu don fuskantar wadannan barazana, inda ya ce makarantun addinin, tare da samun yara masu basira da kuma karfin da suka gada daga tarihi, suna bukatar sabon tsari don fuskantar sauye-sauyen da ke gabatowa.
Memba na Kwamitin ƙoli na Makarantun Addinin Musulunci, ya kuma yi ishara da sabbin bukatun da Juyin juya halin Musulunci ya samar a fannin addini da Tablig, kana kuma ya bayyana cewa nasarar Tablig na dogara ne ga goyon bayan jama'a da kuma iya sarrafa masallatai da kungiyoyin addini da al'umma ke yi. Ya lurar cewa an fara ayyuka na kirkire-kirkire a fannin Tablig wadanda ya kamata a tsara su bisa ga bukatun al'umma tare da hadin gwiwar jama'a.
Your Comment